Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na na Ahlul Baiti (AS) – ABNA– ya habarta cewa: Kafofin yada labarai na cikin gida na kasar Syria sun rawaito cewa, sojojin Isra'ila sun gudanar da bincike tare da kewaya a cikin jiragen sama marasa matuka a saman rufin gidajen mutane a ranar Laraba a yankin Quneitra.
Kutsen na baya-bayan nan na Isra'ila ya zo ne bayan da Syria, Jordan, da Amurka suka amince da wata taswirar hanya a ranar Talata don warware rikicin yankin As-Suwayda da samun kwanciyar hankali a kudancin Syria. Taswirar hanya ta nuna cewa, Washington za ta yi aiki tare da goyon bayan Jordan da kuma tuntubar Damascus don cimma yarjejeniyar tsaro tare da Isra'ila.
Ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Syria ta bayyana cewa, wadannan yarjejeniyoyin juna "sun magance matsalolin tsaron Syria da Isra'ila, tare da tabbatar da 'yancin kan kasar Syria".
Shugaban kasar Siriya Ahmad al-Sharaa ya bayyana -a wata hira da tashar Al-Ikhbariya ta kasar Siriya a kwanakin baya- cewa a halin yanzu kasarsa na tattaunawa kan yarjejeniyar tsaro "domin Isra'ila ta koma inda take kafin ranar 8 ga watan Disamba".
Tun bayan kifar da gwamnatin Bashar al-Assad a ranar 8 ga watan Disamba, 2024, sojojin Isra'ila sun mamaye yankin tuddan Golan, sun mamaye wasu yankuna na Syria, tare da kaddamar da daruruwan hare-hare ta sama kan wuraren soji a fadin kasar ta Syria.
Damascus ta yi Allah wadai da hare-haren da Isra'ila ke ci gaba da yi da kutsawa cikin Quneitra, Daraa, da kuma yankunan Damascus, tare da tabbatar da cewa hakan na kawo cikas ga kokarin tabbatar da zaman lafiya da kuma keta dokokin kasa da kasa da kuma yarjejeniyar raba kasa da kasa ta 1974.
Your Comment